Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-kungiyar ‘yan ta’adda na Da’ish sun mamaye garin Ramadi babban birni a lardin Anbar hakan ya biyo bayan janyewar da sojin Iraki sukayi daga wuraren da suke hannu su.
Kungiyar a ‘yan kwanakin nan tayi amfani da ‘yan kunar bakin wake domin karfafa hare-hare su a kokarin da suke na kama garin.
An dauki sama da shekara daya ana arangama tsakanin sojin Iraki da kungiyar ta Da’ish a garin Ramadi.
Firaministan Iraki Haidar Abadi ya bada dama ga sojin sa kai domin sukai dauki ga rundunar sojin kasar wadanda ahalin yanzu ke filin daga.Abna